Daukar aikin soji: Shin ko rundunar sojojin Najeriya na nuna son kai?

Daukar aikin soji: Shin ko rundunar sojojin Najeriya na nuna son kai?

Hukumar rundunar sojojin Najeriya a jiya ta fito ta karyata rade-raden da ke yawo musamman ma a kafafen sadarwar zamani na cewar wai tana nuna son kai a wajen daukar sabbin ma'aikatan hukumar da ke gudana a halin yanzu.

Babban daraktan rundunar da ke kula da harkokin hulda da jama'a da yada Labarai Birgediya Janar Texas Chukwu shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a garin Abuja.

Daukar aikin soji: Shin ko rundunar sojojin Najeriya na nuna son kai?

Daukar aikin soji: Shin ko rundunar sojojin Najeriya na nuna son kai?

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta karyata Ahmed Salkida

NAIJ.com ta samu kuma cewa daga nan ne sai ya kuma shawarci dukkan 'yan Najeriya da suyi watsi da maganar domin kuwa ana yin ta ne kawai don a bata wa rundunar suna.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi kakkausar suka zuwa ga fitaccen dan jaridar nan da ake kyautata zaton yana da alaka mai karfi da kungiyar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram mai suna Ahmed Salkida game da ikirarin da yayi na cewa yanzu 'yan matan Chibok 15 ne kacal ke da rai.

Fadar shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun babban mai taimakawa shugaban kasar a harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana cewa a gwamnatance wannan labarin kanzon kurege ne kawai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda day a mallaka ga Atiku

2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda day a mallaka ga Atiku

2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda day a mallaka ga Atiku
NAIJ.com
Mailfire view pixel