Kudin makamai: Jihar Bayelsa ta yi barazanar maka gwamnatin Buhari kotu

Kudin makamai: Jihar Bayelsa ta yi barazanar maka gwamnatin Buhari kotu

Gwamnatin jihar Bayelsa dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya ta yi barazanar maka gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari a kotu idan dai har ta dage kan cewa sai ta fitar da kudin siyen makamai har Naira biliyan 360 kafin cire masu kudin su na kaso 13 cikin dari.

Wannan dai ya fito ne daga ofishin kwamishinan yada labarai na jihar Mista Daniel Iworiso-Markson a wata sanarwar manema labarai da ya fitar inda ya ke kara jaddada cewar dole ne sai an biya jihar su kason ta kafin a cire kudin makaman.

Kudin makamai: Jihar Bayelsa ta yi barazanar maka gwamnatin Buhari kotu

Kudin makamai: Jihar Bayelsa ta yi barazanar maka gwamnatin Buhari kotu

KU KARANTA: Tazarcen Buhari: Jiga-jigan APC na shirin fita jam'iyyar

A wani labarin kuma, Tsohon kakakin majalisar wakillai ta Najeriya kuma dan asalin jihar Kano Alhaji Ghali Umar Na'abba ya bayyana cewa shi dai bai ga da wane ido shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai kalli 'yan Najeriya ba har ya ce su sake zabar sa a 2019.

Tsohon kakakin majalisar dai ya ayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da kamfanin jaridar Sun inda ya bayyana takaicin sa ga wadanda yace sun karfafawa shugaban kasar gwiwa don ya sake tsayawa takarar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abu 5 da suka hana APC lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda suka yi a Ekiti

Abu 5 da suka hana APC lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda suka yi a Ekiti

Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti
NAIJ.com
Mailfire view pixel