Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa mijinta baya a 2019

Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa mijinta baya a 2019

Aisha Buhari, uwargidan shugaba Buhari, ta bayyana cewar tayi barazanar kin goyawa Buhari baya idan ya kara tsayawa takara ne saboda kaunar ta da adalci.

Ta ce ba manufarta bace kaskantar da mijinta ko nuna raini ga ofishin shugaban kasa ba.

A watan Oktoban shekarar 2016 ne Aisha Buhari ta jawo hankalin jama'a bayan wata ganawa da jaridar BBC inda take bayyana shakku a kan salon mulkin mijinta, shugaba Buhari, tare da kokwanton sake goya masa baya.

Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa mijinta baya a 2019
Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa mijinta baya a 2019

Shugaba Buhari, ya ce, bashi da masaniyar jam'iyyar da matar sa ke ciki, illa iyaka dai ya san aikinta shine ta tsare masu gidansu na aure, a martanin da ya mayar ga matar ta sa.

DUBA WANNAN: Yiwuwar jingine Osinbajo: APC ta bawa Buhari wuka da nama

Da take jawabi a wurin karramawar da jaridar Vanguard tayi mata, Aisha Buhari, ta bayyana niyyarta ta sake yiwa mijinta yakin neman zabe duk da bata bayyana ko ya zuwa ta gamsu da salon mulkin nasa ba.

'Yan Najeriya sun zabi mijina ne saboda yarda da suka yi da shi. Yana iya bakin kokarinsa wajen hidimtawa Najeriya. Inaso nayi amfani da wannan dama na shaidawa duniya cewar ina goyon bayan mijina a kokarinsa na yin tazarce," inji Aisha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel