Arzikin Mark Zuckerberg ya doshi Dala Biliyan 66 bayan ya amsa sammacin Majalisa

Arzikin Mark Zuckerberg ya doshi Dala Biliyan 66 bayan ya amsa sammacin Majalisa

- Yanzu dai Shugaban Facebook Zuckerberg ya ba Dala biliyan 66 baya

- Dukiyar Mark Zuckerberg ta karu ne bayan hannun jarin sa sun daga

- A makon jiya ne Matashin ya amsa tambayoyi gaban Sanatoci Amurka

Mun samu labari cewa a cikin ‘yan kwanaki kadan Shugaban kamfanin nan na Facebook na sada zumunta watau Mark Zuckerberg ya samu Dala Biliyan 3 wanda idan aka yi lissafi zai haura sama da Naira Tiriliyan guda, a makon da ya gabata.

Idan ba ku manta ba a makon da ya wuce ne Majalisar Amurka ta gayyaci Mark Zuckerberg ya wanke kan sa bisa wasu zargi da ke yawa. CNN Money tace bayan sa’a 10 da Zuckerberg yayi yana amsa tambayoyi sai da dukiyar sa ta karu.

KU KARANTA: Wani bature na neman Shugaban kasa Buhari ya saida masa Najeriya

A farkon makon da ya gabata hajjojin Facebook sun yi kasa, sai dai daga lokacin da Zuckerberg ya bayyana gaban Majalisar Kasar Amurka a Birnin Washington domin gamsar da Duniya kan tsare-tsaren sa hajjojin Facebook su kayi sama.

Mark Zuckerberg dai shi ne ke rike da sama da Miliyan 400 daga cikin hannun jarin Facebook. Hakan ya sa yanzu dukiyar sa ta lula zuwa Dala Biliyan 66. Yanzu haka dai saurayin shi ne na 7 cikin Attajiran Duniya kamar yadda mu ka ji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel