Mutane 3 sun mutu yayin da cutar kwalara ta addabi al'ummar jihar Borno

Mutane 3 sun mutu yayin da cutar kwalara ta addabi al'ummar jihar Borno

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, akalla rayuka uku ne suka salwanta yayin da cutar kwalara ta barke a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana.

Kwamishinan lafiya na jihar Haruna Mshelia ya bayyana hakan ne ga shugaban kungiyar lafiya ta duniya, Tedros Ghebrayesus yayin ziyarar cibiyar su dake birnin Maiduguri a ranar Juma'ar da ta gabata.

Ya ke cewa an samu kimanin mutane 700 da suka kamu da cutar ta kwalara a garin Baga, Doron Baga da kuma Kukawa cikin makonnin da suka gabata.

Mutane 3 sun mutu yayin da cutar kwalara ta addabi al'ummar jihar Borno

Mutane 3 sun mutu yayin da cutar kwalara ta addabi al'ummar jihar Borno

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar kungiyar lafiya ta duniya watau WHO (World Health Organisation) da kuma sauran cibiyoyi tuni sun ƙaddamar da matakai da za su magance cutar a yankunan da ta shafa.

Mista Mshelia ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta kuma gudanar da alluran riga-kafi watanni shidda da suka gabata domin magance cutar.

KARANTA KUMA: Mu na nan akan bakan mu na tafiya yajin aiki a kasar nan - Ma'aikatan Lafiya

NAIJ.com ta fahimci cewa, gwamnatin jihar da tallafin kungiyar WHO sun gudanar da wasu shiri domin magance cututtukan koda, zazzabin cizon sauro, shan inna, kyanda, sankarau da kuma sauran su.

A na sa bangaren shugaban kungiyar WHO Mista Ghebrayesus, ya bayar da tabbaci ga gwamnatin jihar dangane da rawar da za su taka wajen magance cututtuka shan inna, kwalara da sauran su a fadin jihar.

A yayin haka kuma jaridar NAIJ.com ta hikaito yadda cutar kwalara ta salwantar da rayuka 61 a tsakanin watannin Yuni da Dasumba na shekarar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abu 5 da suka hana APC lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda suka yi a Ekiti

Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti

Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti
NAIJ.com
Mailfire view pixel