Dubi kayan abinci da kwastam ta kama a iyakokin Najeriya ana fasa-kwabrinsu

Dubi kayan abinci da kwastam ta kama a iyakokin Najeriya ana fasa-kwabrinsu

- Hukumar custom sun kwace tireloli goma na shinkafa, tare da wasu haramtattun abubuwa na kimanin Naira biliyan 1.6

- Hukumar custom ta kasa ta tare tireloli goma dankare da shinkafa da wasu haramtattun abubuwa na kimanin Naira biliyan 1.6 daga 9 ga watan Maris

- Shugaban custom na zone A ya tabbatar ma da manema labarai a ranar laraba a garin Legas

Dubi kayan abinci da kwastam ta kama a iyakokin Najeriya ana fasa-kwabrinsu
Dubi kayan abinci da kwastam ta kama a iyakokin Najeriya ana fasa-kwabrinsu

Kamar yanda yace, shashin nasu ya samu Naira miliyan 166.20 daga 19 ga watan Maris zuwa 9 ga watan Afirilu. Shugaban hukumar na yankin Comptroller Mohammed Garba yace

Hukumar ta kwace abubuwa da suka hada da hodar ibilis, abubuwan hawa na alfarma guda 64, buhunan shinkafa yar'gwamnati 6,003 (daidai da tireloli goma) kwalaye 963 na naman kaji. Sauran sun hada da jarkoki 431 na man gyada, dila 163 na gwanjo, tayoyi 569,buhunan sukari 69 da kwantainoni guda hudu. Garba yace an kwace sunki 570 da buhuna 98 na hodar ibilis masu nauyin kilogram 1,550 a olorunda na jihar Ogun. Wannan hodar ibilis din tafi kowacce yawa a tarihin miyagun kwayoyin da muke kwacewa a yankin. Wannan miyagun kwayoyin ba karamar ta'asa zasuyi ba Idan suka kai ga mutane.

Wannan miyagun kwayoyin za a mika su ne ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA domin cigaba da bincike.

Kamar yanda ya fada hukumar ta kwaso buhunan shinkafa masu nauyin kilogram 50 guda 2,671 a ma'ajiya guda tara a Ilogbo, Abeokuta.

Shugaban yace ana samun hare hare ga jami'an nasu amma baya hanasu yin aikinsu. Yace ababen hawan guda 64 sun hada da Toyota land cruiser 2018,Escalade 2017 Cadillac ,Range Rover 2014 da Toyota Highlander 2014. Mutane goma aka kama masu alaka da kayan.

DUBA WANNAN: Zamu yi ruwan bama-bamai a Siriya

Yayi jinjina ga shugaban Custom na kasa, Col. Hameed Ali gameda goyon bayan da yake badawa. Haka ma hukumar yan'sanda da sojin Najeriya. Yayi alkawarin hukumar bazasu gaji ba gurin durkusar da bata gari da kuma karawa gwamnati kudin shiga.

A lokacin da kungiyar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta karba hodar ibilis din karkashin jagorancin Mista Lawal Opeloyeru, ya jinjiinawa hukumar custom din. Yayi alkawarin hukumar zata cigaba da bincike. Yace aikin hukumar bazai tafi dai dai ba, ba tare da taimakon hukumar custom din ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel