Dalilin da ya sanya za a gina Gadar Kasa ta N4bn a jihar Kano - Ganduje

Dalilin da ya sanya za a gina Gadar Kasa ta N4bn a jihar Kano - Ganduje

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba, ya bayyana cewa gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta na gina wata katafariyar gadar kasa ta Dangi dake tantagwaryar birnin Kano domin rage cunkoso da jerin gwanon motoci.

NAIJ.com ta fahimci cewa, kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ganawar ranar Larabar da ta gabata da manema labarai a babban birnin kasar nan na tarayya.

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje

Mallam Muhammadu yake cewa, babbar manufa ta wannan gadar kasa ita ce kawo karshen cinkoso gami da rage jerin gwanon motoci a hanyar ta Dangi.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya rashin tsaro ke ci gaba a Najeriya - Wike

Kwamishinan ya kuma yi watsi da sukar wasu daidaikun mutane dake ganin ya kamata a watsar da aikin gadar domin cimma wata manufa ta su ta daban.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan katafaren aiki ya fara kafuwa ne da sanya hannun gwamna Ganduje bayan da ya samu amincewar majalisar zantarwa ta jihar a zaman ta na 111 da ta gudanar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Manyan kalubale 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna

2019: Manyan kalubale 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna

2019: Manyan kalubale 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna
NAIJ.com
Mailfire view pixel