Dalilin da ya sanya rashin tsaro ke ci gaba a Najeriya - Wike

Dalilin da ya sanya rashin tsaro ke ci gaba a Najeriya - Wike

Gwamnan jihar Ribas Mista Nyesom Wike, ya bayyana cewa tsaro a fadin kasar nan ya na ci gaba da tabarbarewa ne a sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC ta zabi siyasantar da da duk wani kalubalen tsaro da ya tunkaro ta.

Gwamnan ya kuma yi kira ga kwararrun masana siyasa da su taka rawar gani wajen bunkasa tare da kawo ci gaba a kasar nan domin tabbatar da gwamnatin tarayya ta sanya kasar nan a turba madaidaiciya.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata yayin da yake karbar bakuncin kungiyar kwararrun 'yan kasuwa da kasafin kudi na kasa ta ICAN a fadar gwamnatin sa dake birnin Fatakwal.

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike

NAIJ.com ta fahimci cewa, gwamnan ya hikaito yadda gwamnatin tarayya ke yiwa rashin tsaro a kasar nan rikon sakainar kashi musamman ta'addanci a garuruwan Taraba, Filato, Kogi, Benuwe, Zamfara, Kwara, Nasarawa, Kaduna, Yobe da kuma Borno.

KARANTA KUMA: Dalilai 7 da za su sanya shugaba Buhari ya yi tazarce a zaben 2019

Gwamnan ya kuma bayyana cikin damuwa yadda gwamnatin tarayya a madadin tunkarar kalubale na ta'addancin garkuwa da mutane a jihar sa sai ta yi yunkurin sanya dokar ta baci.

A yayin haka kuma, shugaban kungiyar ICAN, Alhaji Muhammadu Zakari, ya yabawa gwamna Wike dangane da rawar da ya taka wajen daidaita tattalin arziki a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna
NAIJ.com
Mailfire view pixel