Obasanjo ya kawo cigaba a kasuwancin sadarwa - Dangote

Obasanjo ya kawo cigaba a kasuwancin sadarwa - Dangote

- Shugaban kungiyar Dangote yace kasuwancin sadarwa ya samu cigaba sakamakon tallafin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar

- Dangote yace manufofin gwamnatin zasu iya taimakawa kasuwancin su cigaba ko ya kashesu

- Yace manufar Obasanjo a kan kamfanoni sadarwar shine ya dakatar dasu daga biyan haraji har zuwa lokacin da zasu fara samun riba

Shugaban kungiyar Dangote yace kasuwancin sadarwa ya samu cigaba sakamakon tallafin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar.

A taron ‘yan kasuwa wanda Gateway suka shirya, a kasar Singaphore, Dangote yace manufofin gwamnatin zasu iya taimakawa kasuwancin su cigaba ko ya kashesu. An sanya bidiyon ne ta kafar sadarwa ta Youtube da Facebook a ranar Talata.

Dangote yace manufar Obasanjo a kan kamfanoni sadarwar shine ya dakatar dasu daga biyan haraji har zuwa lokacin da zasu fara samun riba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasa na goyon bayan Buhari game da sake tsayawa takara

Dangote zai halarci taro da ciyaman na Econet wireless da hamshakin dan kasuwar nan, Strive Masiyiwa, a dakin taro na Obasanjo a garin Abeokuta.

Masiyiwa ya bayyana a facebook cewa zasu tattauna game da rayuwa matasan Afirika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi, ya shekara 5 kenan rabonsu da ko waya

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel