Hoho: Malaman makaranta 200 sun shiga taksu

Hoho: Malaman makaranta 200 sun shiga taksu

- Malama makarantar firamare 200 ne ke fuskantar ragin girma a kananan hukumomi hudu dake jihar Anambra.

Yanzu haka idanun wasu baragurmin malaman makaranta ya raina fata, bayan da aka bankado badakalar da suke aikatawa na sayarda littafan makarantar da gwamnatin jihar Anambra ta bayar kyauta domin koyar da yan makarantar firamare.

Malama makarantar firamare 200 ne ke fuskantar ragin girma a kananan hukumomi hudu dake jihar Anambra.
Malama makarantar firamare 200 ne ke fuskantar ragin girma a kananan hukumomi hudu dake jihar Anambra.

Shugaban hukumar ilimin bai daya (UBE) a jihar ne Chief Olisah Nzemeka, ya bayyana hakan, ga manema labarai a jiya Talata a garin Akwa. A cewarsa, baragurbin malaman sun fito ne daga karamar hukumar Idemili ta arewa da Idemili ta kudu da Nnewi ta kudu da kuma Njikoka, sannan yawansu yakai kimanin malamai 200 da suka samu da hannu a cikin badakalar,

"Mun fara binciken ne bayan da muka ji iyayen yara na korafin yadda aka tilasta wa yayansu biyan har Naira 2,200 domin siyan littafin alhali kuma ilimin firamare kyauta ne a Jihar tun shekarar 2017."

KU KARANTA: Wayyo abin tausayi: Wani Mutum ya mutu bayan ya ciro Naira N100,200 daga banki

Yanzu haka dai, shugaban hukumar ya sanya a biya duk iyayen da abin ya shafa kudinsu, ya kuma kara da cewa, ”Wannan aika-aika dai da malaman su kayi, lallai rashin da’a ne ga dokar gwamnati, da kuma saba ka’idar aikinsu. Dole ne su biya duk kudaden da suka karba daga wurin iyayen yaran, kuma zamu bibiyi yadda hakan zai kasance domin tabbata da sun biya.” A cewar Nzemeka

Shugaban hukumar ya kara da cewa, ” A jihar nan ilimi kyauta ne, kuma muna da makarantu fiye da dubu, saboda haka baza mu bar 200 kacal daga cikin malaman su bata mana suna ba. Siyar da irin wadannan littattafan dai an haram ta shi ne tun shekarar da ta gabata, kuma har yanzu muna cigaba da bincike ko akwai sauran wasu baragurbin.”

Nzemeka ya kuma tabbatar da cewa, doka ta basu damar hukunta duk masu yiwa tsarin koyo da koyar kafar ungulu a jihar, a don haka zasu tabbatar an sanya wadanda zasu iya rarraba kayan aikin ba tare da samun matsala a nan gaba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel