Buhari ya nada lauyan Zakzaky a matsayin kwamisinan INEC

Buhari ya nada lauyan Zakzaky a matsayin kwamisinan INEC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Festus Okoye, daya daga cikin lauyoyin Ibrahim Zakzaky, shugaban kungiyar Shi’a a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Okoye na daga cikin mutane 26 da Buhari ya mika sunansu majalisar dattawa domin a tabbatar da su.

A ranar Talata, 10 ga watan Afrilu, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya karanta wasikar bukatar shugaban kasar ga majalisar masu rinjaye.

Okoye wanda ya kasance dan asalin jihar Imo, ya kasance daraktan hukumar kula da hakkin bil’adam. Ya kuma kasance lauya a kotun koli na Najeriya.

Buhari ya nada lauyan Zakzaky a matsayin kwamisinan INEC

Buhari ya nada lauyan Zakzaky a matsayin kwamisinan INEC

A wani hira da akayi da Okoye a shekarar da ya gabata ya bayyana shari’ar Zakzaky a cikin guda biyu da ya fi fuskantar kalubale tunda ya fara aiki shekaru 33 da suka shige.

KU KARANTA KUMA: Buhari: Ba lallai ne shekaru ya zamo kalubale ba a zaben 2019 – Inji Onaiyekan

An kama Zakzaky a shekarar 2015 bayan wasu magoya bayansa sun kara da sojoji a jihar Kaduna.

Yana nan a tsare tun lokacin duk da kiraye-kiraye da ake na a sake shi sannan kuma kotu tayi umurnin sakin nasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta zama gwaman Adamawa

Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta zama gwaman Adamawa

Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta zama gwaman Adamawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel