Rundunar mayakan Soji ta yi caraf da wani kwararren mai hada ma Boko Haram Bama bamai

Rundunar mayakan Soji ta yi caraf da wani kwararren mai hada ma Boko Haram Bama bamai

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da kama da wani kwararre mai hada ma yan Boko Haram bama bamai mai suna Adamu Hassan, a jihar Gombe, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mataimakin Daraktan watsa labaru na aikin Lafiya Dole, Kanal Onyeam Nwachukwu ya sanar da haka a ranar Talata 10 ga watan Afrilu, inda yace Sojojin sun kama Hassan ne a gari Kaltungo, a yayin wani aikin hadin gwiwa da jami’an hukumar DSS.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari (Bidiyo)

Onyeama ya kara da cewa sun kama dan ta’addan, wanda ake yi ma inkiya da suna ‘Baale’ a wani shingen bincike da suka sanya a garin na Kaltungo, kan hanyar Gombe zuwa jihar Yola.

Rundunar mayakan Soji ta yi caraf da wani kwararren mai hada ma Boko Haram Bama bamai
Baale

A wani labarin kuma, Sojoji sun hallaka wasu yan ta’addan Boko Haram guda uku a kauyukan Bokko Hilde da Mujigine na jihar Borno, a ranar 9 ga watan Afrilu, tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda biyu, da babur.

Haka zalika a wani aikin hadin gwiwa tasaknin Sojoji da Sojojin sa kai, sun kama wasu yan Boko Haram da suka fita neman abinci a kauyen Kudiye, dake kan hanyar garin Dikwa zuwa Gulumbagana na jihar Borno, inda ya kara da cewa sun kama su da buhunan hatsi, tsamiya da Babura guda biyu.

Bugu da kari, yan ta’addan sun tabbatar ma Sojoji cewa su yaran shugaban kungiyar Boko Haram ne, Abubakar Shekau, kuma zuwa yanzu suna baiwa Sojoji hadin kai bisa binciken da suke gudanarwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel