Wata kotu a Abuja ta watsawa Sifero Janar Ibrahim Idris kasa a ido

Wata kotu a Abuja ta watsawa Sifero Janar Ibrahim Idris kasa a ido

Wata babbar kotun tarayya dake a garin Abuja babban birnin tarayya ta yi watsi da karar da Sifero Janar na 'yan sandan Najeriya Mista Ibrahim Idris ya shigar a gabanta yana kalubalantar majalisar dattijan Najeriya.

Da yake yanke hukunci game da hakan a jiya, mai shari'a Muhammad Bello ya bayyana majalisar ta dattijai na da hurumin gayyatar Sifeto Janar din domin yayi karin bayani game da al'amurran da suka shafe sa a gaban kwamitocin ta.

Wata kotu a Abuja ta watsawa Sifero Janar Ibrahim Idris kasa a ido

Wata kotu a Abuja ta watsawa Sifero Janar Ibrahim Idris kasa a ido

KU KARANTA: Yan Najeriya mazauna Landan sun yi wa Buhari zanga-zanga

NAIJ.com ta samu cewa tun farko a watannin baya shi Sifero Janar na 'yan sandan Najeriya din ya shigar da majalisar kara a kotu inda yake tuhumar ta da yiwuwar kin yi masa adalci akan rigimar dake tsakanin shi da Sanata Isah Misau.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kebbi dake a shiyyar arewa ta yamma a Najeriya Alhaji Atiku Bagudu a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana yadda yace kasashen duniya musamman ma masu noman shinkafa ke kokarin shiryawa Najeriya gadar zare domin durkusar da ita.

A cewar sa, kasashen dai tun bayan shiga matsin tattalin arzikin da suka yi sakamakon shirin gwamnatin tarayya na wadata kasa da shinkafa, sai suka yanke shawarar karya farashin shinkafar kasar su ta yadda zata iya yin gogayya da wadda ake nomawa a gida Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hoto)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hoto)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel