Tsaro ya tsananta a yayin ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina

Tsaro ya tsananta a yayin ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina

A yayin da aka ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a babbar kotun jihar, tsaro ya tsananta kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tun a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne hukumar hana yiwa tattakin arziki zagon kasa ta EFCC ta shigar da karar tsohon gwamnan har gaban kuliya bisa zargin sa da aikata laifin almundahana ta kimanin Naira biliyan 11.

Tsaro ya tsananta a yayin ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina
Tsaro ya tsananta a yayin ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hadin gambizar jami'an tsaro na DSS, 'yan sanda da Civil Defence, su ne dogarai da suka mamaye farfajiyar wannan kotu yayin sauraron karar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an fara sauraron karar cikin gaggawa yayin da alkalin kotun Mai shari'a Maikaita Bako ya jagorancin zaman ta.

KARANTA KUMA: 2019: Za muyi nasara akan shugaba Buhari - PDP, Accord

Tsohon gwamnan Ibrahim Shema tare da sauran mutane 3 da ake zargi sun hallara a kotun yayin zamanta da suka hadar da; Sani Hamisu Makana, Lawal Ahmad Safana da kuma Ibrahim Lawal Dankaba.

Idan mai karatu zai iya tunawa, kotun a yayin zamanta na karshe da ta gudanar ta kayyade ranakun 10, 11 da kuma 12 na watan Afrilu a matsayin ranakun ci gaba da sauraron karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel