Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wa ‘Yan Boko Haram lugaden wuta

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wa ‘Yan Boko Haram lugaden wuta

- Sojojin kasar nan sun budawa ‘Yan ta’addan Boko Haram wuta a Borno

- Rundunar Sojin Najeriya na sama da kasa ne su ka hadu su ka kai hari

- Sojoji na cigaba da kokarin ganin karshen ‘Yan ta’addan a Yankin Borno

Labari ya zo mana daga babban Jami’in Sojin saman Najeriya Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya cewa Sojojin sama da kasa na Najeriya sun yi wa ‘Yan ta’addan Boko Haram lugaden wuta.

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wa ‘Yan Boko Haram lugaden wuta

Sojojin kasar nan sun lallasa ‘Yan Boko Haram

Sojojin Operation Lafiya Dole sun hada karfi-da-karfi da Rundunar Sojin sama a karshen makon da ya gabata inda su kayi kaca-kaca da ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garuruwan Arege da Tumbun Rago a cikin Jihar Borno.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Rundunar Sojin kasar na sama sun yi amfani da jiragen sama na Alpha-Jet da F-7Ni yayin da wasu Sojojin kuma ke kasa. A haka ne dai aka yi galaba kan ‘yan ta’addan inda da dama su ka mutu yayin da wasu su ka tsere.

Sojojin na Najeriya na cigaba da kokarin ganin bayan ‘Yan ta’addan ne da su ka addabi Yankin Arewa maso gabashin kasar. Yanzu dai an lallasa ‘Yan Boko Haram da ke zaune a Garin Tumbun Rago da kuma Garin Arege.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel