Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II ya bayyana bacin ransa game da yawan sakin mata da maza ke yi, ba tare da basu hakkokinsu ba, inda ya bayyana lamarin tamkar ruwan sha, inji rahoton BBC Hausa.
Sarki ya bayyana haka ne a yayin wani babban taro da aka kaddamar a birnin Yamai dake kasar Nijar, kan hakkin mata a gidajen aure da kuma sha’anin gado, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda Maza suka mayar da sakin Mata kamar ruwan sha na bani tsoro – Inji Sarkin Mata
Sarki ya yi tuni ga shuwagabanni game da nau’o’in nauye nauye da suka rataya a wuyoyinsu, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, ya kara da cewa: “Mu da muke ganin muna zaune da matanmu da Yayanmu suna karatu, idan mun fito mutane suna cewa Allah ya kara maka imani, a duk lokacin da yayanmu suka kai wannan matsayi, jifansu zasu yi.”

Muhammadu Sunusi
Haka zalika Mai martaba ya yi tsokaci game da mummunan halin maza wajen rashin sanin hakkokin aure, inda yace “Abin da ya fi ban tsoro shi ne yadda ake sakin mata da ya’ya, saki a cikin al’ummarmu ya zama kamar ruwan sha.”
Sarki ya koka kan yadda Namiji kawia zai sallami matarsa zuwa gidan iyayenta, ta tattara ta koma gidan iyayent da yaranta, bai san cinta ba, bai san shanta ba, idan kuma iyayen nata basu da hali, shikenan yaran sai du shiga Duniya.
Idan za’a tuna Sarki Muhammadu Sunusi ya sha janyo hankalin jama’a game da matsalolin aure, wanda ra’ayin nasa ya sha janyo cece kuce a tsakanin al’umma, yayin da wasu ke ganin ya na da gaskiya,wasu kuma akasin haka suke yi masa kallo.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com
Source: Hausa.naija.ng