Kamar dai yadda mabanbanta ra'ayoyi ke cigaba da kwaranya game da batun ayyana kudurin sake tsayawa takara da shugaba Muhammadu Buhari yayi a zaben 2019 ranar Litinin din da ta gabata, yanzu hankulan mutane sun raja'a ne zuwa ga wasu 'yan Najeriya da suka nuna sha'awar su ta shugabantar kasar.
Ko shakka babu kuma, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana daga cikin fitattun 'yan siyasar Arewa masu tarin mabiya.

Matakai 3 da Kwankwaso zai iya dauka game da tsake tsayawa takarar tazarcen Buhari a 2019
KU KARANTA: Abun da takarar tazarcen Buhari a 2019 ke nufi
NAIJ.com ta tattaro wasu muhimman matakai da ake tunanin zai iya dauka a yanzu musamman ma ganin cewa shima har yanzu yana jam'iyyar APC.
1. Zai iya tsayawa a jam'iyyar ta APC ya taimaki shugaba Buhari.
2. Zai iya ficewa ya koma jam'iyyar PDP ya tsaya takarar fitar da gwani ya nemi tikitin karawa da Buhari din.
3. Zai iya kafa ta sa jam'iyyar kamar yadda ake rade-rade wadda zai tsaya takara a karkashin ta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Source: Hausa.naija.ng