Hannun jarin sun lula kasa a Najeriya dalilin niyyar tazarcen Buhari

Hannun jarin sun lula kasa a Najeriya dalilin niyyar tazarcen Buhari

- Kasuwar hannun jari yayi kasa a Najeriya a farkon wannan makon

- An samu hakan ne bayan da Shugaba Buhari yace zai sake takara

- An dade ana so a ji matakin da Shugaban kasar zai dauka na 2019

Labari ya zo mana daga kasar waje cewa kasuwar hannun jari sun girgiza kwarai da gaske bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin sa na sake neman takara a zaben 2019.

Hannun jarin sun lula kasa a Najeriya dalilin niyyar tazarcen Buhari

Hannun jari sun yi kasa a Najeriya bayan Buhari yace zai yi takara

Reuters ta rahoto cewa hannu jari a Najeriya sun lula kasa matuka bayan da Shugaba Buhari ya tabbatar da matsayar sa a game da 2019. An dai yi wata-da-watanni ana shirin a ji inda Shugaban kasar ya sa gaba ganin yayi fama da rashin lafiya.

KU KARANTA: Rigimar mu da Buhari ba za ta kare ba - Bukola Saraki

Dama dai hannun jarin na Najeriya ya dan karaya a cikin ‘yan kwanakin nan. Sai dai maganar tazarcen Shugaban kasa Buhari ta sa hannun jarin sun samu muguwar karayar da aka yi sama da watanni uku ba a ga irin sa ba a kasar inji Masana.

Kamar yadda alkaluman tattali su ka nuna, an rasa maki 40, 000 a kasuwar hannun jarin bayan da Shugaban kasar ya rufe wata kafar kila-wa-kala inda ya tabbatar da cewa zai fito takara a zabe mai zuwa wanda ba mamaki ya iya yin nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti

Abu 5 da suka hana APC lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda suka yi a Ekiti

Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben gwamnan Osun kamar yadda ta lashe na Ekiti
NAIJ.com
Mailfire view pixel