Mutane 5 da suka sanya Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019

Mutane 5 da suka sanya Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yana cikin wadanda suka shawarci shugaba Buhari da ya sake tsayawa takara

- Sai shugaban jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed tinubu, ya fada nasa dalilin na cewa, saboda hankalin shugaba Buhari yana a kan magance matsalolin Najeriya a matsayin nasa dalilin

- Ga kuma gwamnoni na jihohi da suma suka bayar da nasu hadin kan game da marawa Buhari baya idan yayi shawarar sake tsayawa takara a zaben 2019

A daidai lokacin da shugaban kasa Buhari ya bayyana kudirinsa na sake takara a 2019, mu kuma mukayi amfani da wannan dama domin binciko wasu daga cikin mutanen da suka karfafa masa gwiwar sake taran.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yace shugaba Muhammadu Buhari yana kokarin cika alkawarin da ya yiwa mutanen Najeriya lokacin zabe, sakamakon haka ya kamata su sake zabarsa a 2019 don cika wadannan alkawura.

Tsohon gwamanan jihar Legas yace dalilinsa na bukatar Buhari ya kara tsayawa takara a zaben 2019, shine saboda hankalin Buhari a koda yaushe yana kan matsalolin dake damun Najeriya da ma Afirika baki daya.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yace yayi farin ciki da mutane ne sukeso Buhari ya cigaba da mulkin kasar nan, ba wai shine yakeso ya cigaba ba, duk da cewa har yanzu bai yanke shawarar cewa zai kara tsayawa ba ko kin tsayawa ba. Yace dani da mutanen kano munyiwa shugaban kasa alkawarin kuri’a 5m a zaben 2019.

Mutane 5 da suka sanya Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019
Mutane 5 da suka sanya Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019

El-Rufa’I ya bayyanawa manema labarai bayan taron gwamnonin APC da suka gudanar, a fadar shugaban kasa, a birnin tarayya, inda yace sun bukaci shugaba Buhari da ya sake tsayawa takara a zaben 2019. Yace ‘yan Najeriya basa nadamar zaben shugaba Buhari haka zalika bazasuyi ba a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 3 da zasu sanya shugaba Buhari sake takara a zaben 2019

Yahaya Bello, gwamnan jihar kogi ya bayyanawa manema labarai cewa, gwamnoni suna bukatar shugaba Buhari ya sake tsayawa takara saboda cigaban da ya kawowa kasar nan, musamman na yaki da cin hanci da rashawa, da kuma rashin tsaro a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel