Jawaban Buratai a lokacin kaddamar da kwamitin bincike akan zargin da TY Danjuma yayiwa hukumar Soji

Jawaban Buratai a lokacin kaddamar da kwamitin bincike akan zargin da TY Danjuma yayiwa hukumar Soji

- Hukumar Sojin ta Najeriya ta jima tana gudanar da ayyukan tsaro a kasar nan, sai gashi ana maganganu akan hukumar a kwanakinnan

- Kungiyoyi daban daban masu zaman kansu ne suka ringa maganganun game da hukumar akan aikin da ta gudanar a jihar Taraba

- Tsohon LT Janar COAS TY Danjuma yana cewa hukumar Sojin ta Najeriya ta hada kai da ‘yan ta’adda tana bari ana yin ta’addanci yanda akaga dama a cikin kasar

Hukumar Sojin ta Najeriya ta jima tana gudanar da ayyukan tsaro a kasar nan, sai gashi ana maganganu akan hukumar a kwanakinnan. Kungiyoyi daban daban masu zaman kansu dana gwamnatin jihar ne suka ringa maganganun game da hukumar akan aikin da ta gudanar a jihar Taraba.

Tsohon LT Janar COAS TY Danjuma yana cewa hukumar Sojin ta Najeriya ta hada kai da ‘yan ta’adda tana bari ana yin ta’addanci yanda akaga dama a cikin kasar, ya bayyana hakane a ranar 24 ga watan Maris, lokacin da yake jawabi a bikin yaye dalibai da akayi a jami’ar ta jihar Taraba.

Wadanda aka zaba an zabesu ne a bisa tabbashin da ake dashi na gaskiyarku, kuma ina da tabbashin cewa zakuyi wannan aiki yanda ya kamata. Na bayarda umurni ga AHQ DAPP dasu wadata ku da duk wasu kayan aiki da zaku bukata don gudanar da wannan aiki yanda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: PMB zaiyi takara a 2019 – Karanta sharhin yan Najeriya kan wannan kudiri na Buhari

Ina bukatar ku zagaya ko ina a jihar ta Taraba kuma ku zanta da masu fada aji a jihar, don ku kawo mana rahoto mai ma’ana. Saboda wannan matsala ce da ta shafi kasa saboda haka nake bukatar ku dauke ta da muhimmanci yanda ya kamata.

Saboda haka a matsayina na shugaban Jami’an Soji, na kaddamar daku a matsayin kungiyar bincike akan zargin da ake yiwa hukumar Soji bisaga aikinda ta gudanar a jihar Taraba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun
NAIJ.com
Mailfire view pixel