Sake tsayawa takara: Na amsa kiran yan Najeriya ne – Shugaba Buhari

Sake tsayawa takara: Na amsa kiran yan Najeriya ne – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya alanta niyyar sake takara zaben kujeran shugaban kasan Najeriya a shekarar 2019.

Shugaban kasan ya bayyana wannan ne a taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da aka gudanar yau Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2018 a sakataiyar jam’iyyar da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wannan mataki da ya dauka amsa kiran yan Najeriya amma ya fadawa masu ruwa da tsakin ne don karramasu.

NAIJ.com ta samu wannan rahoto ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, in da yace: "Shugaban kasan ya ce ya amsa kiran da yan Najeriya ke yi cewa ya sake takara a 2019."

Sake tsayawa takara: Na amsa kiran yan Najeriya ne – Shugaba Buhari

Sake tsayawa takara: Na amsa kiran yan Najeriya ne – Shugaba Buhari

Gabanin bayyana ra’ayinsa, shugaba Buhari ya yi ga ‘yayan jam’iyyar APC su zama tsintsiya madaurinki daya yayinda ake shirin zaben 2018.

KU KARANTA: A dagawa Oyegun kafa – Buhari ya bukaci jam’iyyar APC

Ya bukaci kwamitin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su dagawa Cif John Odigie-Oyegun da mambobin kwamitinsa da suke bukatan sake takara kafa su samu daman sake takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
NAIJ.com
Mailfire view pixel