Wata ‘Diyar Marigayi Abiola za ta tsaya takara a zaben 2019

Wata ‘Diyar Marigayi Abiola za ta tsaya takara a zaben 2019

- Daya daga cikin ‘Ya ‘yan Abiola za ta jarraba farin-jinin ta a zabe mai zuwa

- Rinsola Abiola ta bayyana cewa za tayi takara a zaben 2019 idan lokaci yayi

- Marigayi Abiola ya mutu ne a kurkuku bayan yayu ikirarin lashe zaben kasar

Mun samu labari daga gidan Talabijin na OAK cewa wata daga cikin ‘Ya ‘yan babban ‘Dan siyasar kasar nan Marigayi Mashood K. Abiola za ta tsaya takara a zaben kasar nan mai zuwa watau na 2019.

Wata ‘Diyar Marigayi Abiola za ta tsaya takara a zaben 2019

‘Diyar Marigayi Mashood Abiola za ta fito takara

Rinsola Abiola a wajen wani taro da bayyanawa Duniya cewa za ta fito takarar siyasa a 2019. Ko da yake dai har yanzu ba mu san kujerar da ‘Diyar gawurtaccen ‘dan siyasar za ta nema ba, amma ta tabbatar da cewa da ita za ayi.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai kama hanyar zuwa Landan

Misis Rinsola Abiola dama dai tana cikin manyan ‘Yan Jam’yyar APC mai mulki na Majalisar BOT ta amintattu. Bayan nan kuma Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya nada ta a cikin masu ba shi shawara a Majalisar.

Budurwar ta nuna rashin gamsuwar ta da yadda ba a ba mukamai a Jam’iyya. ‘Diyar Abiola tace ta san cewa akwai tsada da kashe kudi neman tsayawa takara a Najeriya amma duk da haka za ta jarraba sa’ar ta da farin jinin ta a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu
NAIJ.com
Mailfire view pixel