Rundunar sojin Najeriya sun kawar da harin kunar bakin wake 2 a Borno

Rundunar sojin Najeriya sun kawar da harin kunar bakin wake 2 a Borno

Rundunar sojin Najeriya sun kawar wani mumunar harin kunar bakin wake da wasu yan Boko Haram sukayi kokarin kaiwa Konduga, jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Jami’an tsaron sun hallaka yan kunar bakin waken ne yayinda sukayi kokarin shiga garin da daren jiya.

NAIJ.com ta samu wannan rahoto ne a jawabin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, inda yace:

“A wani harin yaki da ta’addaci na ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu 2018, rundunar sojin Operation Lafiya Dole masu yawo a Konduga sun hallaka yan kunar bakin wake wadanda sukayi kokarin shiga garin Mandanari a Konduga, jihar Borno.

Yan kunar bakin waken guda 2 dauke da bama-bamai na hanyar shiga garin misalign karfe 8 na dare, inda jami’an tsaro suka hangosu kuma suka kawar da su.

Jami’an tsaron suka bude musu wuta kawai sai suka tayar da bama-baman. Yan kunar bakin waken ne kawai suka rasa rayukansu yayinda wasu mutane 3 suka ji kananan raunuka.”

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 149 daga hannun Boko Haram, sun damke yan ta’adda 5

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin Laftanan Janar Tukur Buratai sun ceto mutane 149 daga hannun yan ta’addan Boko Haram a mabuyarsu.

A wannan hari an hallaka yan Boko Haram 3 kuma an damke 5.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ma’aikatan Najeriya za su shiga yajin aiki gadan-gadan

Ma’aikatan Najeriya za su shiga yajin aiki gadan-gadan

Ma’aikatan Najeriya za su shiga yajin aiki gadan-gadan
NAIJ.com
Mailfire view pixel