Wani Mahaifi ya garkame dan sa har na tsawon shekaru 20 a kasar Japan

Wani Mahaifi ya garkame dan sa har na tsawon shekaru 20 a kasar Japan

Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, wani Mahaifi ya shiga hannun hakuma a ranar Asabar ta yau da laifin garkame dan cikin sa mai cutar hauka har na tsawon shekaru 20 a Yammacin kasar Japan.

Jami'an na 'yan sanda sun yi ram da wannan mahaifi mai shekaru 73 a duniya, Yoshitane Yamasaki da laifin garkame dan sa wanda a yanzu shekarun sa na haihuwa 42 kamar yadda Kakakin su ya bayyanawa manema labarai a birnin Sanda na garin Hyogo.

Sai dai kakakin ya bayyana cewa, har yanzu babu wani cikakken bayani dangane da wannan lamari a sakamakon bincike da ya ke ci gaba da wakana.

Rahotanni sun bayyana cewa, mahaifin ya garkame dan na sa a wani keji na katako mai tsayin kafa 3.3, sai kuma fadi da bai wuci mita 1.8 ba.

KARANTA KUMA: Hotunan Sabbin Dakarun Sojin Sama 195 da aka yaye a garin Kaduna

Mahaifin dai ya bayyana cewa ya aikata hakan a sakamakon tabuwar hankali da dan na sa ke fama da ita. Ya kuma bayyana cewa ya kan ciyar tare ba shi damar yin wanka a kowace rana.

A halin yanzu dai wannan da da aka sakaya sunan shi yana karbar kulawa a asibiti sakamakon cutar lankwasar kashin baya da ya kamu da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel