Gwamnatin tarayya za ta gina sabuwar matatar mai a Najeriya

Gwamnatin tarayya za ta gina sabuwar matatar mai a Najeriya

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da amincewar ta a kan gina sabuwar matatar mai da iskar gas watau Liquefied Petroleum Gas extraction plant (LPG) a takaice a jihar Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya nan ba da dadewa ba.

Bangaren dake kula da albarkatun man fetur da iskar gas na kasar ne dai ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a garin Abuja.

Gwamnatin tarayya za ta gina sabuwar matatar mai a Najeriya
Gwamnatin tarayya za ta gina sabuwar matatar mai a Najeriya

KU KARANTA: Iyalan Gwamnan Kogi sun tsallake rjya da baya

Legit.ng ta samu cewa a cewar mai jami'in hulda da jama'a na bangaren, gwamnatin ta yanke shawarar baiwa kamfanin Green Energy International Limited kwangilar yin aikin biyo bayan cika sharrudan da yayi da kuma kyakkyawar alakar su da gwamnati.

A wani labarin kuma, Mahukunta a hukumar nan dake kula da kamfanonin albarkatun man fetur na NNPC mallakin gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun sanar da bayar da kwangilar shimfida bututan mai har biyu zuwa Arewa.

Wadannan bututan man dai kamar yadda muka samu za su farfado da masana'antu da kuma tattalin arzikin arewacin kasar nan idan har aka kammala su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel