An kama shi ya daskaras da gawar mahaifiyarsa na tsawon shekaru 3 don yaci gaba da karabar fanshonta

An kama shi ya daskaras da gawar mahaifiyarsa na tsawon shekaru 3 don yaci gaba da karabar fanshonta

- Yan sandan kasar Indiya sun kama wani mutum wanda ya ajiye gawar mahaifiyarsa a cikin firinji har na shekaru uku

- Mutumin ya ajiye gawar mahaifiyarsa ne don ya rika amfani da zanen yatsan hannun ta wajen karban fansho

- Bincike ya nuna cewa mahaifiyar mai shekaru 87 ta rasu ne sakamakon bugawar zuciya tun 2015

Yan sandan kasar Indiya sun kama wani dan shekaru 43 a garin Kolkata daya ajiye gawar mahaifiyarsa a cikin firinji har na tsawon shekaru uku yana amfani da zanen yatsar hannunta yana karban fanshon ta. Asirin sa ya tonu ne yayinda Yan sanda suka gano gawarta a gidansa ranar Alhamis.

Ya ajiye gawar mahaifyarsa na tsawon shekaru 3 don ya cigaba da karban kudinta na fansho
Ya ajiye gawar mahaifyarsa na tsawon shekaru 3 don ya cigaba da karban kudinta na fansho

A yayinda yake zantawa da jaridar Indian Express, mataimakin kwamishinan yan sanda Nilanjan Biswas yace, "An ajiye gawar Bina Mazumdar ne a cikin firinji tun shekarar 2015. Muna cigaba da binciken dalilin da yasa aka ajiye gawar ta."

KU KARANTA: Matasan arewa sunyi gargadi mai tsanani ga Obasanjo kan sukar gwamnatin Buhari

Yan sandan sun kuma ce wanda ake zargin, Subhabrato Mazumbar yana tsare kuma za'a cigaba da bincike kafin a gurfanar dashi. Wata majiya daga yan sandan ta bayyanawa cewa mahaifiyar mai shekaru 87 da rasu ne a dalilin buguwar zuciya.

Kafin rasuwarta, Bina ma'aikaciyar gwamnati ce a hukumar Abinci na indiya amma daga baya tayi murabus. Bayan rasuwar ta Subhabrato ya cigaba da karban fansho Rs 50,000 a kowane wata kuma mahaifinsa yana da masaniya kan lamarin.

Subhabrato dalibi ne mai karantar fasahar jima da kuma yana sayar da fata. Yan sanda sun gano takardan shedar cewa Bina tana raye amma na bogi ne. Daga baya ma bincike ya nuna cewa Subhabrato yana da tabin hankali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel