Akwai dimbin ayyukan gwamnati shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Akwai dimbin ayyukan gwamnati shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

- Shugaban ma'aikata na kasa Winifred Oyo-Ita tace gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu cigaba da dama a watannin da suka gabata

- Tace kafafen yadda labarai suna rage abubuwa da dama a cikin abubuwan cigaba da Buhari ya kawo a kasar nan

- Oya-Ita ta bukaci a karawa ma’aikatar labarai da al’adu kudade don gudanar da ayyukansu yanda ya kamata

Akwai dimbin ayyukan shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Akwai dimbin ayyukan shugaba Buhari da ba'a bayyanawa - Oyo-ita

Shugaban ma'aikata na kasa Winifred Oyo-Ita tace gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu cigaba da dama a shekaru biyu da suka gabata suka gabata, wadanda ba’a bayyanawa mutane ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Oyo-Ita ta bayyana cewa kafafen yadda labarai suna rage abubuwa da dama cikin abubuwan cigaba da Buhari ya kawo a kasar nan, a ranar Alhamis 5 ga watan Afirilu a birnin tarayya, lokacinda suka kai ziyara ga sakatarorinma’aikatar labarai da al’adu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa a karkashin shugaban ma'aikatan sun kirkira Sakatarorin bangarorin ma’aikatar ne don inganta ayyukan bangarorin maikatar na (MDAs). Oya-Ita ta bukaci a karawa ma’aikatar labarai da al’adu kudade don gudanar da ayyukansu yanda ya kamata

Oya-Ita ta gargadi gidajen Talabijin masu nuna finafinan yara da cewa suyi taka tsan-tsan, saboda akwai wadanda ke koyawa yara madugo da luwadi. Ta kumayi jinjina ga Satariyar ma’aikatar Grace Gekpe akan kokarin da tayi wurin samun 94% na kasafin ma’aikatar a shekarar 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Daura ya roki shugaba Buhari ya sake duba batun Peace Corp

Sarkin Daura ya roki shugaba Buhari ya sake duba batun Peace Corp

Sarkin Daura ya roki shugaba Buhari ya sake duba batun Peace Corp
NAIJ.com
Mailfire view pixel