'Yan sanda sun tsinto gawawwaki 10 a yankunan jihar Benuwe

'Yan sanda sun tsinto gawawwaki 10 a yankunan jihar Benuwe

Hukumar 'yan sanda ta jihar Benuwe ta bayyana cewa, a ranar yau ta Juma'a ta tsinto gawawwaki 10 na wasu kauyawa da ake zargin 'yan ta'adda sun raba su da rayuwar su a kauyukan Tse-Audu da Enger na karamar hukumar Gwer ta Yamma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan rahoto da sanadin kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, ASP Moses Yamu, inda ya bayyana cewa gawawwakin mutanen da harin ranar Alhamis ne ya ritsa da su a kauyukan.

Yake cewa, jami'an tsaro dake gudanar da aikin su na sintiri a garin Naka su ne suka yi ruwa da tsaki wajen kwasar wannan gawawwaki.

'Yan sanda sun tsinto gawawwaki 10 a yankunan jihar Benuwe

'Yan sanda sun tsinto gawawwaki 10 a yankunan jihar Benuwe

Kakakin ya ci gaba da cewa, gawawwaki 10 jami'an suka tsinto cikin wani Daji dake tsakanin kauyukan Tse-Adu da Enger na karamar hukumar ta Gwer.

KARANTA KUMA: Faruwar wasu ababe 3 a watan Maris da suka tashi hankalin dandalan sada zumunta

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, karamar hukumar Gwer ta Yamma ta sha fama da rikicin tsakanin makiyaya da manoma a shekarun 2012 da kuma 2014.

NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar Sojin Sama ta yaye sabbin Soji 195 a makarantar horaswa dake garin Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Da duminsa: Kwankwaso ya fitar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel