Rayuwa a matsayinka na dalibi a makarantar Boko Haram

Rayuwa a matsayinka na dalibi a makarantar Boko Haram

Tsokaci daga Edita: Marubuciyar, Fatima Bukar ta tunatar kan yadda Maiduguri yake kafin zuwan ta’addanci da ya maida babban birnin Borno wajen zubar da jini, hawaye da kuma bakin ciki. Ta kara da bayyana irin nasarori da rundunar sojin Najeriya ta samu wajen yakar ta’addanci.

Maiduguri ta kasance babban birnin jihar Borno a Arewa maso Gashin Najeriya ta samu dawo ta cigaba da gudanar da al’amuranta nay au da kullum.

Rayuwar ta kasance mai sauki ga dalibi a garin Maiduguri, wanda hakan yasa dalibai ke zuwa daga ko’ina a fadin Najeriya.

Zuwan kungiyar masu fada da sunan addini ta Boko Haram a karkashin jagorancin Abubakar Shekau, wanda shine magajin shugaban kungiyar na farko Muhammed Yusuf, ya lalata komai game da rayuwa wanda mutane ke jin dadinsa a garin Maiduguri.

Duka da kokarinda jami’an tsaro keyi bai hanasu cigaba da ta’addanci a jihohin Arewa maso Gashin Najeriya ba kamar su, Borno, Yobe, da Adamawa ba, har gara ma zuwan shugaban Sojin Najeriya na yanzu Tukur Buratai shine aka da samu sauki.

KU KARANTA KUMA: Abun tausayi: Wata yar gudun hijira ta bayyana halin da suka shiga tare da iyalinta bayan barinsu gida

An kashe dubunnan mutane sakamakon haka, wanda ya zama hari sosai ga mutane harda dalibai, bin haryar ta Maiduguri a shekarun 2014 zuwa 2016, wanda haka yasa dalibai dayawa suka koma wasu jami’o’in da fadan bai shafi jihar da suke ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel