Kotu ta daure tsohuwar shugabar kasar Korea ta kudu kan laifin cin hanci da rashawa

Kotu ta daure tsohuwar shugabar kasar Korea ta kudu kan laifin cin hanci da rashawa

-An daure tsohuwar shugabar kasar ta Korea ta kudu Park Geun-hye na tsawon shekaru 24 sakamakon kamata da akayi da laifin cin hanci

-Park mai shekaru 66 bata samu halartar kotun ba a ranar juma’a lokacin da aka yanke mata wannan hukunci, sakamakon rashin lafiya

-Park nada damar daukaka kara daga nan zuwa sati daya akan wannan hukunci na cin hanci da aka sameta dashi

An daure tsohuwar shugabar kasar ta Korea ta kudu Park Geun-hye na tsawon shekaru 24 sakamakon kamata da akayi da laifin cin hanci.

Park mai shekaru 66 bata samu halartar kotun ba a ranar juma’a lokacin da aka yanke mata wannan hukunci, sakamakon rashin lafiya da take fama dashi tun watan Oktoba.

Park nada damar daukaka kara daga nan zuwa sati daya akan wannan hukunci na cin hanci da aka sameta dashi.

Mai gabatar da kara yace shekara 30 aka yanke da kuma tarar £80m akan wanda aka samu da aikata cin hanci.

KU KARANTA KUMA: Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye

Mai gabatar da karar ya sameta da laifuka 18, kuma yace Park ta hada kai da tsohon abokinta Choi Soon-sil wurin karbar cin hanci na £25 daga hannun abokan hurdar kasar Korea ta Kudun, wanda suka hada da Samsung da kuma Kamfanin Lotte don samun dama daga gwamnatin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel