Mun kara kudin Jirgin kasa ne saboda masu kudi sunfi talakawa amfani dashi - Amaechi

Mun kara kudin Jirgin kasa ne saboda masu kudi sunfi talakawa amfani dashi - Amaechi

- Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yace dalilin kara kudin sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Birnin Tarayya ne saboda masu kudi ne sukafi amfani dashi

- Amaechi yace niyyar shugaban kasa a kan wannan hanyar sufuri ta jirgin kasa shine don a dauki talakawa

- Ministan ya karfafawa mutane gwiwa dasu cigaba da la’akari da kokarin da gwamnati keyi akansu, kuma yace shine mutum na farko da zai fara sani idan wata matsala ta samu injin jirgin

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yace dalilin kara kudin sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Birnin Tarayya ne saboda masu kudi ne sukafi talakawa amfani dashi.

Amaechi yace niyyar shugaban kasa a kan wannan hanyar sufuri ta jirgin kasa shine don a dauki talakawa.

Zamu kara kudin Jirgin kasa saboda masu kudi sunfi talakawa amfani dashi - Amaechi

Zamu kara kudin Jirgin kasa saboda masu kudi sunfi talakawa amfani dashi - Amaechi

“A kowane inji na jirgi muna kashe N56m, bayan muna karbar N600 daga hannun mutane, abunda muke samu shine N16m, ma’ana munawa masu kudi kyautar N40m kyauta a kowane wata.

“Idan ka duba zaka ga cewa talakawa kalilan ne amfani da jirgin, yanzu haka idan kaje Rigasa zakaga motocin manyan mutane an aje sunbi jirgi, shiyasa muka kara kudin jirgin”.

KU KARANTA KUMA: Babu kifin roba a Najeriya – Hukumar NAFDAC

Ministan ya karfafawa mutane gwiwa dasu cigaba da la’akari da kokarin da gwamnati keyi akansu, kuma yace shine mutum na farko da zai fara sani idan wata matsala ta samu injin jirgin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel