Sayen makamai: Naira biliyan 360 ta kamfe din Buhari ce a 2019 - PDP

Sayen makamai: Naira biliyan 360 ta kamfe din Buhari ce a 2019 - PDP

Jam'iyyar adawa babba kuma tsohuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya PDP ta zargi gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da shirya ma 'yan Najeriya gadar zare musamman ma game da kudin makaman da shugaba Buhari ya ware don sayen makamai.

Jam'iyyar ta PDP dai ta zargi cewa kudaden da suka kai Naira biliyan 360 jam'iyyar ta APC na shirin yin anfani ne da su domin gudanar da abubuwan da suka shafi ayyukan jam'yya da kuma kamfe din zabukan 2019.

Sayen makamai: Naira biliyan 360 ta kamfe din Buhari ce a 2019 - PDP

Sayen makamai: Naira biliyan 360 ta kamfe din Buhari ce a 2019 - PDP

KU KARANTA: Amarya a Bauchi ta yi shagalin bikin bazata

NAIJ.com ta samu cewa wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in yada labarai na jam'iyyar ta Peoples Democratic Party, PDP Mista Kola Ologbondiyan ya fitar a Abuja.

Haka ma dai Alamu dai na kara nuna cewa da alama batun sayen makaman nan na makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 360 da shugaba Buhari ya amince ayi da su za su kara kawo rikici tsakanin fadar shugaban kasar da kuma majalisar dattijai.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya fara fitowa karara ne a ta bakin Sanata Ben Bruce da ke wakiltar mazabar jihar Bayelsa a zauren inda ya bayyana cewa Buhari bai da ikon sayen makaman har sai majalisar ta amince masa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel