Gwamnati na ba ta da kudurin taimakon wani addini - Shugaba Buhari

Gwamnati na ba ta da kudurin taimakon wani addini - Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din nan a fadar sa dake a garin Abuja ya ayyana cewa shi fa gwamnatin da yake shugabanta ba ta da buri ko kudurin taimako ko kuma fifita wani addini a kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin addinin Kirista daga yankin arewacin Najeriya dake da rajin tabbatar da samuwar zaman lafiya karkashin jagorancin Bishop John Abu Richard.

Gwamnati na ba ta da kudurin taimakon wani addini - Shugaba Buhari
Gwamnati na ba ta da kudurin taimakon wani addini - Shugaba Buhari

Legit.ng ta samu cewa haka zalika shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa za ta cigaba da aiki tukuru domin kyautatuwar rayuwar dukkan 'yan Najeriya ba tare da kallon banbancin addini, kabila ko yare ba.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ayyana ware kimanin makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 100 domin aiwatar da gyaran hanyar da ta tashi daga Kano ta nufi Gwarzo har zuwa Dayi na karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina.

Shugaban hukumar nan dake yin ayyukan gyaran hanyoyi ta gwamnatin tarayya watau Federal Road Maintenance Agency (FERMA) na shiyyar Kano Injiniya Adedayo Adebayo shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel