Bikin aure: Wata amarya ta zabi yi wa marasa lafiya galihu maimakon shagulgula a Bauchi

Bikin aure: Wata amarya ta zabi yi wa marasa lafiya galihu maimakon shagulgula a Bauchi

A wani mataki mai cike da karsashi da Allah-san-barka, wata amarya diyar daya daga cikin manyan manajojin kamfanin albarkatun man fetur na NNPC mai suna Aisha Bala-Wunti ta zabi baiwa marasa lafiya musamman ma marasa galihu kiwon lafiya kyauta a bikin ta maimakon shagulgula.

Da take karin haske game da shirin, amaryar ta bayyana cewa an dauko tawagar likitocin ne daga kasar Indiya kuma kwararri ne a dukkan fannonin kiwon lafiya musamman ma a matakin farko.

Bikin aure: Wata amarya ta zabi yi wa marasa lafiya galihu maimakon shagulgula a Bauchi
Bikin aure: Wata amarya ta zabi yi wa marasa lafiya galihu maimakon shagulgula a Bauchi

KU KARANTA: Yan fashi na sata yanzu haka a garin Offa, jihar Kwara

Legit.ng ta samu cewa amaryar ta bayyana cewa ta zabi ta yi hakan ne a maimakon shagulgulan da aka saba yi a lokutan bukukuwan Aure domin samun karin kusanci ga Allah da kuma tabbatuwar albarkar auren da za ta yi.

A wani labarin kuma, Jama'ar gari sun dan shiga cikin rudani biyo bayan wata zanga-zangar lumana da mata masu ciki su kimanin 200 suka yi a garin Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Alhamis 5 ga watan Afrilu.

Majiyar mu dai ta shaida mana cewa daruruwan matan dai an gan su kowace da ciki niki-niki suna ta faman kwankwami da cancakwato yayin da kuma suka tare hanyar shiga da fita na asibitin kwararrun garin na Akure.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel