Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Adamu Garba II yace zai doke Buhari a zaben dan takarar jama’iyyar ta APC

- Adamu yace tsayawarsa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ba wai kamfen bane ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Adamu ya bayyana cewa cancantarsa ce zatasa ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta APC

Mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Adamu Garba yace, ba gudu ba ja da baya akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta APC.

Yace saboda yafi kowa cancanta a jam’iyyar, inda yace zai doke shugaba Buhari a zaben dan takarar jam’iyyar na wannda zasu bawa tikiti a zaben 2019.

Adamu Garba ya kara da cewa ya zabi zam’iyyar ne saboda yana ganin cewa ita kadai ce jam’iyyar da zata bawa matasa dama. Ya bayyana haka ne a wurin wani taro a jihar Legas, lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Garba yace yana hanyoyi da dama wadanda zaiyi amfani dasu ya maganace matsalolin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Jam’iyya: Gwamna El-Rufai yayi kaca-kaca da manyan Gwamnonin APC

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa an nemi ayi baram-baram a taron da Gwamnonin Jam’iyyar APC su kayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A wajen taron Shugaban Gwamnonin APC ya bayyana cewa sun goyi bayan a cire John Oyegun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel