Shehu Sani ya nuna rashin amincewar shi akan kudin da Buhari ya bayar domin sayen makamai

Shehu Sani ya nuna rashin amincewar shi akan kudin da Buhari ya bayar domin sayen makamai

- A ranar Larabar nan ne data gabata Ministan Tsaro na kasa Mansur Dan Ali, ya sanar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada izinin sayen makamai na kimanin dala biliyan daya, domin tabbatar da tsaro da kuma yaki da masu tada kayar baya a kasar nan

- To sai dai kuma Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi magana akan kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a bayar domin yaki da rashin tsaro a kasar

Shehu Sani ya nuna rashin amincewar shi akan kudin da Buhari ya bayar domin sayen makamai
Shehu Sani ya nuna rashin amincewar shi akan kudin da Buhari ya bayar domin sayen makamai

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi magana akan kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a bayar domin yaki da rashin tsaro a kasar nan.

A ranar Larabar nan ne data gabata Ministan Tsaro na kasa Mansur Dan Ali, ya sanar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada izinin sayen makamai na kimanin dala biliyan daya, domin tabbatar da tsaro da kuma yaki da masu tada kayar baya a kasar nan.

DUBA WANNAN: Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

Da yake magana akan kudin a shafin sa na Twitter, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar sayan makaman a halin yanzu bashi da wani amfani. Ya ce kamata yayi gwamnati ta tabbatar da lafiyar jami'an tsaro da kuma jin dadin su kafin tayi tunanin sayo makamai.

"Cire kudi masu uban yawa haka domin sayen makamai bashi da ma'ana, idan bamu damu da lafiyar sojojin mu ba da kuma jin dadin su, sannan kamata yayi a bawa wadanda suka ji rauni a cikin su kudi na musamman domin magani, a taimakawa iyalana wadanda suka mutu a fagen yaki, a dauki nauyin karatun 'ya'yansu. Don haka a halin yanzu ba sayen makamai ya kamata gwamnati tayi ba," in ji shi.

Har ila yau Sanatan yace, muna bukatar mu tunatar da kanmu cewar masana'antun mu na makamai duk sun mutu, dan haka kamata yayi ace muyi kokarin gyara namu ba wai muje mu azurta wasu kasashen ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel