Hukumar ‘Yan Sanda sun rusa kamfanin da ake hada bindigogi a jihar Ebonyi

Hukumar ‘Yan Sanda sun rusa kamfanin da ake hada bindigogi a jihar Ebonyi

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Edo ta bayyana cewa ta wargaza wani kamfani da ake hada bindiga a jihar

- Hukumar ta gano tarin makamai 146 wadanda aka hana yin amfani dasu da harsasai a hannun wadanda basu da izinin rike wadannan makamai

- Kwamishinan ‘Yan Sandan, Titus lamorde, yace an gano makaman ne bayan umurnin da shugaban hukumar ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris ya bayar ga duka ma’aikatun hukumar na kasa

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Edo ta bayyana cewa ta wargaza wani kamfani da ake hada bindiga a jihar.

Hukumar ta gano tarin makamai 146 wadanda aka hana yin amfani dasu da harsasai a hannun wadanda basu da izinin rike wadannan makamai.

Hukumar ‘Yan Sanda sun rusa kamfanin da ake hada bindigogi a jihar Ebonyi
Hukumar ‘Yan Sanda sun rusa kamfanin da ake hada bindigogi a jihar Ebonyi

Kwamishinan ‘Yan Sandan, Titus lamorde, yace an gano makaman ne bayan umurnin da shugaban hukumar ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris ya bayar ga duka ma’aikatun hukumar na kasa, inda yace ayi kokarin tattara duk wasu makamai daga wannun mutane wadanda doka bata basu izinin rike makaman ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kuma dai, wani sanatan Najeriya ya sake mutuwa

Lamorde yace, hukumar ta kafa kwamiti wanda mataimakin kwamishinan ‘Yan Sandan ya jagoranta, Oyeyemi Oyediran.

Lamorde ya kara da cewa hukumar ta wargaza kamfanin bindigogin ne wanda yake a Mgbo, a karamar hukumar Ohaukwu a jihar.

Kwamishinan ya shawarci wadanda ke rike da makan a hannunsu har yanzu dasu gaggauta kawowa hukumar kafin a bincikosu, don za’a hukuntasu idan aka kamasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel