Kotu ta wanke dan Gaddafi daga zargin aikata kisa

Kotu ta wanke dan Gaddafi daga zargin aikata kisa

- Kotun daukaka kara ta wanke daya daga cikin yaran tsohon shugaban kasar Libiya Muammar Gaddafi akan zargin kisa

- Saadi Gaddafi, wanda ya dade a tsare a babban birnin Tripoli tunda aka tsareshi a kasar Niger a shekarar 2014

- An gane cewa bashi da laifi a kan zargin da ake masa na bautantar, da barazana, da kisan tsahon dan wasan kwallon kafar Riyani

Kotun daukaka kara ta wanke daya daga cikin yaran tsohon shugaban kasar Libiya Muammar Gaddafi a kan zargin da ake masa na kisan dan was an kwallon kafa kafin rikicin daya barke a kasar a 2011 kamar yadda ma'aikatar shari'a na kasar ta bayyana.

Saadi Gaddafi, wanda ya dade a tsare a babban birnin Tripoli tun bayan da aka karbo shi daga kasar Nijar a shekarar 2014. An gane cewa bashi da laifi a kan zargin da ake masa na bautantar, da barazana, da kisan tsahon dan was an kwallon kafa, Bashir Riyani.

Kotu ta wanke dan Gaddafi daga zargin aikata kisa
Kotu ta wanke dan Gaddafi daga zargin aikata kisa

KU KARANTA: Jami'ar Bayero zata bude gidajen talabijin da rediyo

Ma’aikatar Sharia' na kasar tace Saadi tara har na kudaden kasar Libiya Dinari 500 ($377) kuma an bashi wa’adin shekara daya a gidan wakafi, bisa ga laifin shan giya a shekarar 2006.

Kafin rasuwar shugaba Gaddafi, Sa'ad ya kasance dan wasan kwallon kafa ne kuma kwamandan Soji na musamman, Sai dai kuma har yanzu yana fuskantar tuhuma a Tripoli da keda alaka da rigimar NATO ta 2011.

Ya gudu zuwa kasar Nijar, a lokacin da ake rikicin, sauke mahaifinsa daga mulki kafin a kasheshi. Daya daga cikin yaran Saadi yace zai daukaka kara a kan hukuncin da aka yankewa mahaifinsa a ranar Talata.

Bayan haka kotun babban birnin Libiyan ta yankewa wani kuma cikin yaran Gaddafin hukuncin kisa, Saif al-Islam, da wasu jami’ai na waccan gwamnatin. An dade ana tsare da Saif al-Islam a yammacin birnin Zintan amma a halin yanzu ba'a san inda yake ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel