‘Yan siyasan da ka iya kawowa Shugaba Buhari cikas a zaben 2019

‘Yan siyasan da ka iya kawowa Shugaba Buhari cikas a zaben 2019

Wannan karo kuma mun kawo maku wani harsashe ne da mu kayi na wasu ‘yan siyasa da mu ke tunanin su na iya tsayawa takarar Shugaban kasa da Muhammadu Buhari idan har ya fito takarar a zabe mai zuwa na 2019.

‘Yan siyasan da ka iya kawowa Shugaba Buhari cikas a zaben 2019

Ba mamaki Shugaba Buhari zai kuma takara a 2019

Ga dai jerin ‘yan takarar nan kamar haka:

1. Rabiu Kwankwaso

Ba abin mamaki bane idan har Kwankwaso ya tsaya takarar Shugaban kasa a APC kamar yadda yayi a 2014. Duk da zai yi wahala takara da Shugaba Buhari amma zai yi matukar wahala Kwankwaso yayi nasara a 2023 lokacin da ake sa rai ‘Dan kudu yayi mulki.

KU KARANTA: Abubuwan da za su hana Kwankwaso mulkin Najeriya

2. Bukola Saraki

Da dama daga cikin ‘Yan Majalisar kasar har a cikin ‘Yan Jam’iyyar PDP na kokarin tunzura Bukola Saraki ya fito takarar Shugaban kasa. Saraki dai ya dade yana harin kujerar sai dai har yanzu yana nuna cewa bai da niyyar takara da Buhari.

3. Aminu Tambuwal

Kwanakin baya Gwamnan na Sokoto yayi wani taro da ‘Yan PDP a Kudancin Najeriya. Wasu na ganin akwai masu ingaza tsohon Shugaban Majalisar kasar ya fito takara. Shi ma dai ya tabbatar da cewa ba zai nemi kujerar Shugaba Buhari ba duk da sanin gobe sai Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan

Ambariyan ruwa yaci hanyar kauyen su tsohon shugaban kasa Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel