2019: Basarake yana neman jama'a su sake zaben Shugaba Buhari

2019: Basarake yana neman jama'a su sake zaben Shugaba Buhari

- Sarkin Kasar Egba yayi kira ga Jama'a su sake zaben Shugaba Buhari

- Babban Sarkin yace akwai bukatar Buhari ya kammala aikin da ya fara

- Oba Adedotun yace Buhari Shugaba be mai gaskiya da manufofin kirki

Alake na kasar Egbaland watau mai martaba Oba Adedotun Gbadebo ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci a sake zaben sa 2019 domin karasa ayyukan da ya faro.

2019: Basarake yana neman jama'a su sake zaben Shugaba Buhari

Alake na kasar Egba yace Shugaba Buhari na da manufa

Labarin da mu ka samu daga Jaridun kasar nan shi ne Oba Adedotun Gbadebo ya nemi mutanen kasa su marawa Shugaba Buhari baya a 2019 lokacin da wata Kungiyar 'Yan siyasa karkashin Orji Uzor Kalu ta kai masa ziyara a fadar sa.

KU KARANTA: Al-Mustafa ya bayyana yadda aka kashe Sani Abacha

Sarkin na kasar Yarbawa ya bayyana cewa Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da kuma tsarin gyara kasa don haka yace ba za su bari wani Shugaba ya karbi mulki hannun sa ba ya tsaida duk manufofin da Shugaban kasar ya dauko.

Mai martaba Oba Adedotun Gbadebo yace shi da kan shi yana cikin masu yakin neman Shugaba Buhari ya zarce domin idan har Shugaban ya tafi, to wani ne dabam zai zo ya kawo wasu tsare-tsare na dabam da su ka sabawa na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

NAIJ.com
Mailfire view pixel