Cin zarafin ƙananan yara: Kotu ta garkame wani Mutumi daya kwashe shekaru 7 yana zakke ma ɗiyar matarsa

Cin zarafin ƙananan yara: Kotu ta garkame wani Mutumi daya kwashe shekaru 7 yana zakke ma ɗiyar matarsa

Wani mutumin banza mai suna Oluwadare Joseph, dan shekara 42 dake yi ma diyar matarsa fyade ya gamu da fushin Kotu bayan Alkali ya bada umarnin a garkame shi a gidan Yarin Kirkikiri.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun majistri, B.O Osunsanmi ne yayi watsi da bukatar wanda ake tuhuma da aikata laifin na neman Kotu ta bada belinsa, inda ya umwarci a garkame shi har sai ya samu shawara daga babban jami’in shigar da kara na jihar Legas.

KU KARANTA: Bashin naira Triliyan 4.2: Majalisun dokokin Najeriya na gab da watsa ma Buhari kasa a ido

Ana tuhumar Joseph ne da zakke ma diyar matarsa, wanda yake rikewa a matsayin diyarsa, tun bayan da ya auri mahaifiyarta, wanda ya kwashe shekaru 7 yana fyadeta a gidansu dake unguwar Meiran na jihar Legas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara, ASP Ezekeil Ayorinde yana cewa a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2018 ne Joseph ya dinga yi ma yarinyar Fyade, tun tana yar shekara 9 har lokacin da ta kai shekaru 16.

“yana dukanta tare da yin barazanar kashe ta a duk lokacin da ta yi kokarin hana shi hadin kai, ta kai kararsa wajen mahaifiyarta, amma bata dauki wani mataki ba game da hakan. Daga nan sai yarinyar ta tsere, bayan kwana biyu da uwarta ta nemeta bata ganta bane, sai ta ka kara Caji Ofis.” Inji Dansanda.

Jim kadan sai yarinyar ta bayyana, inda ta shaida ma Yansanda dalilin tserewarta, wannan ne dalilin da ya sabbaba kama mijin mahaifiyarta. Laifin ya ci karo da sashi na 137 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, kamar yadda Dansandan ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel