Gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye da kudaden data karba daga hannun wadanda suka dibi kudaden al’umma – Timi Frank

Gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye da kudaden data karba daga hannun wadanda suka dibi kudaden al’umma – Timi Frank

- Bayanai game da wadanda suka debi kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba da gwamnatin tarayya keyi ya kawo kace nace tsakanin jama’ar kasar nan

- Sakataren kungiyar APC, Kwamrad Timi Frank, ya bayyana nasa ra’ayin akan jerin sunayen

- Kwamrad Frank yanaso gwamnatin tarayya ta cigaba ta bayyana sunayen wadanda suka maido da kudade kuma ta fada ko nawa aka mayar

Sakataren jam’iyyar APC na tarayya Kwamrad Timi Frank, ya kalubalanci gwamnatin tarayya data bayyana sunayen wadanda suka debi kudin gwamnati da kuma nawa aka maido domin sanar da al’umma abunda gwamnati take ciki da kuma yanda take gudanar da al’amuranta.

A wani bayani da aka turawa NAIJ.com a ranar Talata 3 ga watan Afirilu, Kwamrad Frank yace, abu ne mai kyau a sanarwa al’umma yanda al’amuran gwamnati ke gudana don magance yaduwar cin hanci a kasar nan.

Sakataren ya bukaci gwamnatin data tuna irin alkawarurrukan data yiwa mutane a shekarar 2015 lokacin da take yakin neman zabe.

Gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye da kudaden data karba daga hannun wadanda suka dibi kudaden al’umma – Timi Frank

Gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye da kudaden data karba daga hannun wadanda suka dibi kudaden al’umma – Timi Frank

Bayan haka tsohon Sakataren harkoki na ma’aikatar wutar lantarki, Godknows Igali, yayi ikirarin cewa an lababa sunansa ne a cikin wadanda suka debi kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba wanda gwamnatin tarayya ta fitar.

KU KARANTA KUMA: Fitaccen malamin addini a jihar Bauchi ya yi hadari tare da iyalansa

Ya karyata rahotanni game da zargin da ake masa akan N7bn da aka gano a hannun daya daga cikin mutanensa, ya kara da cewa ba a karbi ko sisi daga hannunsa ba, kawai an makalashi ne a cikin jerin sunayen dan an san yana cikin mutanen Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya

An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya

An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya
NAIJ.com
Mailfire view pixel