Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya

Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya

- Farashin mai ya tashi a kasuwar Duniya.

- Burin Najeriya na samun kudade ya fara cika

A yanzu haka dai farashin gangar danyan mai ya daga a sakamakon rage haƙo man da Amurka tayi da kuma tsammanin ko za'a sake ƙaƙabawa kasar Iran takunkumi .

Shugaban sashin kasuwanci na OANDO a yankin Asia, ya ce, "Sakamakon rashin tabbas kan dawo da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran, bisa yarjejeniyar makamin kare dangi tsakanin Amurka da Iran" da kuma raguwar hako mai da aka samu daga kamfanonin hakar mai na Amurkan ne ya haddasa tashin farashin.

A baya dai ana dillanci ganga guda ne a dalar Amurka $65.1 inda yanzu ya koma $65.18.

KU KARANTA: Jerin barayin kasa: Sharrin Gwamnatin APC ne Inji Sanata Stella Oduah

Farfadowar farashin man dai na da alaka da dakatar da yawan man da ake hakowa da kasar Rasha da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) su kayi, a shekarar da ta gabata (2017) domin rage yawan man a kasuwa don farashin nasa ya daga.

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja
NAIJ.com
Mailfire view pixel