Sauyi: Kasar Saudiyya za ta bude wurin shakatawa da mata za su rika yawo 'tsirara'

Sauyi: Kasar Saudiyya za ta bude wurin shakatawa da mata za su rika yawo 'tsirara'

Sakamakon kokarin samar da sauye-sauye a bangaren dodkin kasar daular musulunci ta Saudiyya, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya bayyana kudurin gwamnatin masarautar kasar na bude wajen shakatawa na musamman inda mata za su iya yawon su a tsirara.

Sai dai mun samu cewa masarautar ta bayyana cewa wannan wajen zai zama kebantacce ne ta yadda mata ne kadai za su je wajen kuma a wurin za su iya saka kayan wanka ba tare da sun rufe jikin su ba.

Sauyi: Kasar Saudiyya za ta bude wurin shakatawa da mata za su rika yawa 'tsirara'

Sauyi: Kasar Saudiyya za ta bude wurin shakatawa da mata za su rika yawa 'tsirara'

KU KARANTA: Henry ya musulunta bayan wa'azin Izala ya ratsa shi a Abuja

NAIJ.com ta samu cewa tuni har masarautar ta ayyana tare da ware wani bangare na tekun bahar maliya dake a kan iyakar kasar ta bangaren arewa maso yamma domin yin hakan.

A wani labarin kuma, Yayin da kasar Saudiyya ke ta dada kara shiga cikin cakwakiyar rikicin addini sakamakon kokarin kawo sauye-sauye a kasar da Yarima Mohammed bin Salman ke yi, ya bayyana cewa shi a kasar sa yanzu babu sauran banbanci a tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni.

Yariman yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da wata jaridar Atlantic a nahiyar turai inda yake ziyarar aiki tun satin da ya shude.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya

An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya

An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9 a Somaliya
NAIJ.com
Mailfire view pixel