Budurwa ta kashe kanta a Jigawa

Budurwa ta kashe kanta a Jigawa

- Rundunar ƴan-sanda ta ƙasa reshen Jihar Jigawa, ta tabbatar da rahotan mutuwar wata budurwa a jiya Litinin

- Budurwar dai ta sha maganin kwari ne mai guba wato fiya-fiya.

Kakakin rundunar ƴan-sanda na jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ne ya shaidawa manema labarai a babbabn birnin Jihar wato Dutse, cewa, a jiya Litinin ne al'amarin ya faru a karamar hukumar Birnin Kudu.

"Labari ya iske mu cewa, wata yarinya ƴar shekara 17 mai suna Gambo, ta sha fiya-fiya har ta fita daga haiyacinta an kaita babban asibitin birnin kudu, nan take muka tura jami'ai don bincike, amma sai dai kash, da isarsu sai suka tarar har ta mutu." Jinjiri ya fada.

KU KARANTA: Mutane 3 da sunan su ke cikin barayin Najeriya sun fitar da kan su

Ya kara da cewa, tuni sun miƙa gawarta ga ƴan-uwan marigayyar don yi mata sutura.

Kakakin rundunar ya kuma tabbatar da cewa zasu fara bincike domin gano musabbabin mutuwa wannan budurwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo

Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo

Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel