Dattawan Arewa ku sani cewa Buhari bashi da na biyu a zaben 2019 - Kungiyar Siyasa

Dattawan Arewa ku sani cewa Buhari bashi da na biyu a zaben 2019 - Kungiyar Siyasa

- Kungiyar magoya bayan cigaban siyasa sun fadawa Dattawan Arewa cewa Buhari dashi da wata dama ta kin tsayawa takara a zaben 2019

- Kungiyar ta fadi hakan ne saboda tana ganin cewa babu wani wanda za’a tsaida takara wanda ya fishi cancanta

- A kokarin da Dattawa da masu ruwa da tsaki a Arewa sukeyi na neman wanda zasu tsaida takara wanda yafi Buhari cancanta

Kungiyar magoya bayan cigaban siyasa sun fadawa Dattawan Arewa cewa Buhari kokarin da suke na neman dan takara a zaben 2019, suna wahalar da kansu ne kawai wanda karshe abun zai zama cinikin biri a sama.

Kungiyar ta fadi hakan ne saboda tana ganin cewa babu wani wanda za’a tsaida takara wanda yafi Shugaba Muhammadu Buhari cancanta.

Bayan taron da Dattawan suka gudanar a ranar Asabar, a birnin tarayya, inda sukace da Buhari da ‘Yar’adua duk ‘yan arewa ne, wadanda cancantarsu tasa manyan ‘yan siyasa suka zabosu ba wai ‘yan Arewa suka zabesu ba.

Dattawan Arewa ku sani cewa Buhari bashi da wata dama a zaben 2019 - Kungiyar Siyasa
Dattawan Arewa ku sani cewa Buhari bashi da wata dama a zaben 2019 - Kungiyar Siyasa

A ranar Lahadi, lokacin zantawa da manema labarai a birnin tarayya, Ciyaman na kungiyar magoya bayan cigaban siyasar (NAF) Malam Gidado Ibrahim, yace, neman da akeyi na dan takara wanda yafi Shugaba Buhari cancanta zai zama bata lokaci ne kawai.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kungiyar Boko Haram ta kai hari Maiduguri sun kashe mutane 15 tare da raunata wasu 55

Ibrahim yayi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yadda su bata kudirin Shugaban Buhari na gayar kasar nan su mayar damu zuwa ga mulkin wadanda ke satar kudin al’umma.

Ya kara da cewa lokacin satar kudin gwamnati da sunan siyen makamai yak are, gashi dama an tsabatace bangaren man fetur na kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel