Wasu gungun yan bindiga sun kai mummunna hari a kauyen Tsohuwar gari dake karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka hallaka mutane guda biyu tare da sace mutane 9, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yan bindigan sun far ma kauyen ne da misalin karfe 12 na rana, inda suka kai harin ga jama’an kauyen, daga cikin wadanda suka kashe har da wata sabuwar Amarya.
KU KARANTA: Matsalar tsaro a Zamfara: Sanata Kabiru Marafa yayi kira da a tsige gwamna Adul-Aziz Yari
Sai dai, Allah yayi ma wasu mutane guda uku gyadar doguwa, inda suka tsere daga hannun maharan, amma sauran mutane shiddan basu samu tserewar ba. Guda daga cikin wadanda suka tseren yayi ma majiyarmu karin haske:
“Da misalin karfe 12 na rana ne suka far mana a kauyen tsohuwar gwari, a daidai bakin farin Kwarita, inda masu siyar da magungunan gargajiya ke tallace tallacensu, haka zalika kauyen bashi da hanya mai kyau, don haka ne yan bindigan ke amfani da hanyar wajen tare duk wanda suka gani a hanyar. A nan ne suka tare mu, suka bindige mutum biyu, suka kuma sace mutum tara.” Inji shi.
Da aka tuntubi Kaakakin rundunar Yansanda jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar harin, sai dai bai yi dogon bayani game da lamarin ba.
Idan za’a tuna, a baya ma wasu yan bindiga da ake zargin yaran tsohon shugaban yan bindigan jihar Zamfara ne, Buharin Daji, sun kashe Sojoji guda 11 a karamar hukumar Birnin Gwari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com
Source: Hausa.naija.ng