Shin ko zaku iya tuna rayuwar Shahararren Magini Muhammadu Durugu na garin Zazzau

Shin ko zaku iya tuna rayuwar Shahararren Magini Muhammadu Durugu na garin Zazzau

Garin Zazzau ba zai taba mance wa da shahararren Maginin nan ba da rayu a karni na 19, Muhammadu Duguru, wanda ya shahara da sunan Babban Gwani, sakamakon fice da kuma kwarewa akan sana'ar sa ta gine-gine.

Mutanen Najeriya musamman na yankin Arewa ba za su mance da wannan mutum ba da Allah ya ba shi baiwa ta fasahar iya tsara tsayayyen gini.

Shin ko zaku iya tuna rayuwar Shahararren Magini Muhammadu Durugu na garin Zazzau
Shin ko zaku iya tuna rayuwar Shahararren Magini Muhammadu Durugu na garin Zazzau

A garin Zazzau kadai, da yawan mutane sakamakon girmamawa da suke yiwa Babban Gwani, ya sanya suke cewa duk ginin da ba na shi ba to bai dace ya amsa sunan gini ba.

A sakamakon sharara a daular Sarakuna da masu hannu da shuni na wancan zamani, tarihi ya bayyana cewa, Babban Gwani shi ya taka rawar gani a wasu gine-ginen masallatai da fada a biranen Kano, Katsina, Bauchi da kuma Zaria.

KARANTA KUMA: Jerin 'yan Siyasa 10 mafi tarin dukiya a Najeriya

Bankade-banaden jaridar Legit.ng ta bayyana cewa, mafi sharar gini da Babban Gwani ya yi a lokacin rayuwar sa shine ginin Masallacin Juma'a na garin Zazzau da kawowa yanzu yake ci gaba da bayar da sha'awa ga masallata.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta bayar da lambar yabo ga gwamnatin jihar Kaduna a sakamakon rawar da take takawa wajen inganta harkokin kasuwanci da habakar tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel