- Kungiyar hadin kan Najeriya wadda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta fadawa ‘Yan Najeriya su tsoraci gwamnatin Buhari
- Kungiyar a cikin wani jawabi na tsohon Ministan tsaro Lt. Gen. Theophilus Danjuma ta zargi hukumar Soji da hadin kai da wasu mutane wurin sakin wadanda aka samu da laifi
- Shuwagabannin tsaro na kasa sun zargi wasu kungiyoyin mutane da shirye-shirye game da kawo tangarda a zaben 2019

Zaben 2019: Kuyi takatsantsan da gwamnatin Buhari - Sakon Obasanjo ga 'yan Najeriya
Kungiyar hadin kan Najeriya wadda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta fadawa ‘yan Najeriya su tsoraci gwamnatin Buhari saboda ta gurbata hukumomin tsaro na kasar nan, a gabanin zaben 2019 mai zuwa.
DUBA WANNAN: An damke wasu 'yan kungiyar asiri da ake dade a nema ruwa a jallo
Kungiyar ta bayana cewa a wani jawabi na tsohon ministan tsaro, Lt. Gen. Theophilus Danjuma (rtd.), yace hukumar Soji na hadin kai da wasu mutane wurin sakin wadanda aka kama masu laifi.
Darakta Janar na hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya, Mr. Lawal Daura da na hukumar bincike ta tarayya, Mr. Ahmed Rufa’i, tare da shugaban tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin, sunyi korafi a kan cewa wasu kungiyoyin mutane suna shirin kawo tangarda game da zaben 2019.
Osuntoki ya fadawa daya daga cikin manema labaran jaridar Punch cewa shuwagabannin jami’an tsaro suna yin abinda jam’iyyar APC ta sanyasu da kuma garruruwan kabilar shugaban kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Source: Hausa.naija.ng