Rikita-Rikita: An ce 'yan majalisar tarayya su maida makudan kudaden da suke ansa

Rikita-Rikita: An ce 'yan majalisar tarayya su maida makudan kudaden da suke ansa

Wata kungiya dake rajin tabbatar da mulkin adalci da kuma tabbatauwar Demokradiyya da kuma kare hakkin dan adam wadda ba ta gwamnati ba watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) a takaice ta yi kira ga 'yan majalisun tarayyar Najeriya da su gaggauta maida kudaden da suke ansa.

Wannan dai kamar yadda suka ce ya biyo bayan kwarmaton da Sanata Shehu Sani yayi inda ya fallasa cewa 'yan majalisar na dattawa na karbar akalla Naira miliyan 13 da rabi duk watan duniya domin gudanar da ayyukan yau-da-kullum.

Rikita-Rikita: An ce 'yan majalisar tarayya su maida makudan kudaden da suke ansa

Rikita-Rikita: An ce 'yan majalisar tarayya su maida makudan kudaden da suke ansa

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe wani jigon jam'iyyar APC

NAIJ.com ta samu kuma cewa daga baya bayan matsin lamba sosai, hukumar da ke kula da kayyade alawus alawus din jami'an gwamnati ta bayyana cewa abun da ya kamata su rika ansa dai bai fi Naira miliyan 1 ba.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin kula da harkokin aikin hajji watau National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) a turance ta sanar da kara wa'adin yin rijista ga maniyyata aikin hajjin na bana shekarar 2018 ya zuwa karshen watan Afrilu mai zuwa.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai dauke da sa hannun jami'ar hulda da jama'a ta hukumar ta fitar mai suna Hajiya Fatima Mustapha Muhammad.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron shugaban APC daga makaranta

Yan bindiga sun yi garkuwa da karamin yaron shugaban jam’iyyar APC na jahar Borno

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yaron shugaban APC daga makaranta
NAIJ.com
Mailfire view pixel